"Za mu sanar da wanda zai gaje ta cikin makonni biyu ko uku masu zuwa, ko kuma nan ba da jimawa ba," Trump ya fadawa 'yan jaridu a lokacin da yake sanar da yin murabus din Nikki Haley a gaban idonta.
"Muna da mutane masu yawa wadanda suke son yin wannan aikin," in ji Trump.
Haley za ta ci gaba da kasancewa a kan wannan mukami har zuwa karshen shekarar nan, wanda zai cika shekaru biyu da fara aikinta a wannan matsayi. Trump ya fada cewa dama Haley ta sanar da shi tun watanni 6 da suka wuce game da aniyarta na yin murabus din.
"Ban tsara wani abu dangane da inda nake son komawa ba" in ji tsohuwar gwamnan South Carolina a lokacin da ta shedawa manema labarai.
Haley, mai shekaru 46 da haihuwa, an tabbatar da ita ne a matsayin jakadar kasar Amurka a MDD tun bayan rantsar da shugaba Trump a watan Janairun 2017. Ana kallonta a matsayin daya daga cikin na hannun daman mista Trump da suke dasawa. (Ahmad Fagam)