in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Jaridar Financial Times: Ba wanda zai ci moriya daga yakin ciniki
2018-10-04 19:57:47 cri
Shahararren mai sharhi kan batun tattalin arziki na jaridar "Financial Times" ta kasar Birtaniya Martin Wolf, ya rubuta wani bayani wanda aka wallafa shi a jiya Laraba, inda ya ce ra'ayin da shugaban kasar Amurka Donald Trump ya dauka, na ganin cewa kasar Amurka za ta ci nasara a yakin cinikin da kasar ke yi da kasar Sin kuskure ne, domin ba wanda zai ci moriya daga wannan takkadama.

A cewar Wolf, shugaba Trump ba ya kallon batun yakin cinikin da idon basira, musamman ma a fannoni 2: Na farko shi ne ya dauki wata babbar kasa domin takkadama da ita, sa'an nan na biyu, yana kallon kasar Amurka a matsayin wata kasa mai cikakken karfin tattalin arziki, har ma zatonsa ya wuce gaskiya. (Bello Wang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China