in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
UN ta jinjinawa dakarun shirinta na wanzar da zaman lafiya da suka rasa rayukansu yayin da suke bakin aiki a Sudan ta Kudu
2018-05-30 09:19:31 cri
Shirin wanzar da zaman lafiya na MDD dake aiki a Sudan ta Kudu, ya jinjinawa jami'ansa da suka rasa rayukansu a bakin aiki, wajen kare rayuka da kokarin dawo da zaman lafiya a kasar mafi kankantar shekaru a duniya.

Da yake jawabi yayin ranar jami'an wanzar da zaman lafiya ta MDD karo na 70 a birnin Juba, mataimakin wakilin musaman na Sakatare Janar na MDD, kuma shugaban shirin wanzar da zaman lafiya a Sudan ta Kudu, David Shearer, ya ce jami'an wanzar da zaman lafiya na fuskantar kalubale da dama a Sudan ta Kudu, amma duk da haka, suna jurewa, tare da ci gaba da bada goyon baya ga burin wanzar da zaman lafiya a kasar.

A don haka ya ce, su ke makokin abokan aikinsu, misali wadanda harin Mali na baya-bayan nan ya rutsa da su, da na Jamhuriyar Afrika ta Tsakiya da ma Sudan ta Kudu. Haka zalika, ya ce suna tunawa da jami'an UNMISS 55 da suka mutu a shekarar 2011.

David Shearer, ya ce hakkin shirin ne, kare rayukan fararen hula da taimakawa wajen wanzar da zaman lafiya mai karko a Sudan ta Kudu. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China