Mataimakiyar Sakatare Janar na MDD Amina Mohammed ce ta yi kiran yayin wani muhimmin taron kan Dafur da aka yi a gefen babban taron zauren majalisar na bana
Amina Mohammed ta ce an zuba kudi dala billiyan 16 ga aikin wanzar da zaman lafiya cikin shekaru 10 da suka wuce, baya ga kudaden da aka kashe ga ayyukan jin kai domin rage radadin da jama'a ke fuskanta. Ta ce yayin da yankin ke farfadowa daga yaki, lokaci ya yi da za a karfafa nasarorin da aka samu, tana mai cewa lokaci ya yi da ya kamata a dauki matakin tabbatar da yankin Dafur ya samu ingantuwa ta fuskar tsaro da ci gaba.
Tun a shekarar 2003 yakin basasa ya barke a yankin, abun da ya yi sanadin mutuwar dubban mutane tare da raba wasu kusan miliyan 2 da matsugunansu. (Fa'iza Mustapha)