Wadannan alkaluma a cewar wannan rahoto an samu karuwar da kaso 7 cikin a fannin tafiye-tafiye da kuma karuwar kaso 5 cikin 100 kan kudaden da ake kashewa bisa shekarar da ta gabace ta.
A cewar hukumar kula da harkokin yawon shakatawa ta MDD, adadin masu bulaguro a duniya zai haura biliyan 1.8 nan da shekarar 2030. Ana kuma ganin kasuwar harkokin yawon shakatawar kasar Sin za ta kasance mafi saurin bunkasa a duniya kana za ta taka muhimmiyar rawa wajen raya bangaren na yawon shakatawa.(Ibrahim)