Darakta Janar na hukumar zabe ta kasar Essosse Erik, ya bayyanawa taron manema labarai da aka yi a birnin Yaounde cewa, baya ga wasu rumfunan zabe da aka kada kuri'a bisa tsari na tsaro a yankunan arewa maso yammaci da kudu maso yammacin kasar saboda yanayin da ake ciki a wuraren, an kada kuri'a ba tare da wata matsala ba a kasar da ma kasashen waje, yana mai cewa kawo yanzu, babu kiddidigar da za ta nuna adadin mutanen da suka kada kuri'a a sauran sassan duniya.
Nan take bayan kammala kada kuri'ar, ofisoshin hukumar na yankuna suka fara kirgen kuri'un da kowanne dan takara ya samu.
Hukumar zaben ta ce kimanin mutane 6,600,000 ne suka yi rejista a zaben na jiya Lahadi. (Fa'iza Mustapha)