in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
IRC ta ce kasar Sin ta bada dimbin gudunmuwa ga aikin samar da kayakin jin kai
2018-09-30 16:25:42 cri
Shugaban kungiyar agaji ta duniya Red Cross, Peter Maurer, ya ce kasar Sin ta taimaka gaya wajen daidaita ayyukan samar da agajin jin kai ga al'ummomi.

Yayin wata tattaunawar da aka yi da shi a gefen babban taron zauren MDD karo na 73, Peter Maurer, ya jinjinawa tallafin da kasar Sin ke bayarwa ga kasashen dake fuskantar barazanar yaki da rikice-rikice.

Ya kara da cewa, ayyukan da kasar Sin ke yi karkashin shirin wanzar da zaman lafiya na MDD a wurare masu haddura babbar gudunmuwa ce.

Har ila yau, ya ce cikin shekaru da dama, kungiyar ta kan horar da jami'an wanzar da zaman lafiya kafin su fara aiki, domin horon na yin kyakkyawan tasiri gare su a fagen daga, yana mai cewa abu mafi muhimmanci shi ne yadda horon ke tabbatar da kare rayukan jami'an.

Peter Maurer ya ce yana jin dadin ganin yadda jami'an kasar Sin ke kara shiga ana damawa da su cikin ayyukan wanzar da zaman lafiya na MDD, wanda ke nuna irin rawar da kungiyar ke takawa a fagen daga a matsayin mai shiga tsakani. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China