in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Peng Liyuan Ta Gabatar Da Jawabi Kan Batun Shawo Kan Cutar Tarin Fuka A MDD Ta Bidiyo
2018-09-28 08:09:10 cri

Sannunku abokai, Suna na Peng Liyuan, jakadiyar hukumar lafiya ta duniya (WHO) game da yaki da tarin fuka da cutar kanjamau, ina muku gaisuwa da kuma taya ku murnar shirya wannan taro.

Na zama jakadiyar yaki da cutar tarin fuka ta kasar Sin ne a shekarar 2007, kana jakadiya ta fatan alheri a shekarar 2011. Wannan wani babban nauyi ne da kullum nake kokarin ganin na sauke. Yau kusan sama da shekaru 10, a kowace ranar 24 ga watan Maris din kowace shekara, na kan ziyarci al'ummomin dake fama da cutar tarin fuka, domin na ilimantar da su, ta yadda za su canja halayensu da kara daukar matakan magance wannan cuta. A wannan shekara na ziyarci lardin Hubei dake tsakiyar kasar Sin, inda na sanar da matasa dalibai wasu muhimman bayanai game da cutar tarin fuka da yadda za su zauna cikin koshin lafiya, sannan na sanar da su muhimmacin yin tsafta. Na kuma gamu da wani mutum a wani kauye wanda ya murmure daga cutar, inda na karfafa masa gwiwar zama mai kamfel din yaki da cutar ta yadda zai sanar da mutane da dama game da matakan yaki da cutar.

Yayin wannan rangadi na kuma halarci wani biki da aka shirya domin karrama masu kamfel din yaki da wannan cuta, galibinsu suna aiki ne a yankunan karkara, kuma suna da dimbin labarai da ma kwarewa da za su bayar.

Bari na ba ku wani labari game da Shili, wata ma'aikaciyar lafiya daga lardin Sichuan, kuma daya daga cikin ayyukan da take yi shi ne kula da masu fama da cutar tarin fuka. A lokacin da mummunan girgizar kasa ta afkawa lardin Sichuan a shekarar 2008, garinsu na daga cikin wadanda Iftila'in ya shafa, sai dai duk da mummunan barnar da girgizar kasar ta yi, ta yi kokarin tuntubar masu fama da tarin fuka 540 da take kula da su, tana shafe mila-milai don ganin ta kula da wadannan marasa lafiya, ta kuma shafe kwanaki 20 tana ba da magunguna ga masu fama da wannan lalura. A matsayinta na likita ta san muhimmancin shan maganin cutar tarin fuka kamar yadda ake bukata. Bukatarta ta biya, dukkan mutane 540 dake fama da cutar tarin fuka sun warke tsaf. Wannan ba karamar nasara ba ce.

Ina son na yi amfani da wannan dama wajen godewa kafofin watsa labarai da masu ba da goyon baya gami da masu aikin sa-kai dubu 700 a shirye-shiryen yaki da cutar tarin fuka a kasar Sin, mun taimaka wajen ilimantar da sama da kaso 75 cikin 100 na al'ummar kasar Sin game da cutar tarin fuka. A sakamakon haka, an yi nasarar ceto rayukan jama'a. Kuma ni shaida ce kan irin nasarar da aka samu a shirye-shiryen yaki da cutar tarin fuka a kasar Sin. Godiya ga magungunan da muke samarwa kuma za mu ci gaba da samar da magunguna da jinya mai inganci a kan lokaci.

A wasu yankunan, yanzu haka yaki da tarin fuka, ya kasance muhimmin bangare na shirin yaki da talauci, inda aka yi nasarar warkar da masu fama da cutar da dama, kana yawan mace-mace sanadiyar cutar ta kara raguwa.

A duk lokacin da na kai ziyara kasashen waje, na kan yi kokarin sanya batun cutar tarin fuka a cikin ajanda ta. Ina matukar farin cikin ganin yadda masu fama da cutar tarin fuka ke samun taimakon da suke bukata. Wannan ya samu ne sakamakon hadin gwiwar gwamnatoci, da kungiyoyin kasa da kasa da kungiyoyi masu zaman kansu, kwararru da masu aikin sa-kai. Sai dai kuma har yanzu akwai tarin kalubale, tarin fuka yana daga cikin cututtuka masu barazana ga rayuwar dan-Adam. Matsalar isassun kudade da hanyoyin magance cutar, na daga cikin manyan matsalolin da ake fuskanta a duniya.

Hukumar lafiya ta duniya WHO ta riga ta kaddamar da matakan yaki da cutar tarin fuka, don haka lokaci ya yi da za a dauki matakan da suka dace. Ina kira ga kowa da kowa da ya shiga a dama da shi a kokarin da muke na inganta rayuwar miliyoyin jama'a dake fama da cutar tarin fuka da ma kawo karshen cutar baki daya a duniya.

Ina fatan wannan taro zai samu nasara.

Na gode.

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China