in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
MDD ta yi maraba da shirin sake fasalin tattalin arzikin Libya
2018-09-20 11:02:12 cri
Shirin wanzar da zaman lafiya na MDD a Libya UNSMIL, ya yi maraba da matakin sauya tsarin tattalin arziki da Gwamnatin Libya ta dauka.

Sanarwar da shirin UNSMIL ya fitar, ta yi maraba da matakin da majalisar koli ta kasar ta dauka bayan ta tuntubi babban bankin kasar, na fara aiwatar da shirin sauya tsarin tattalin arziki.

Sanarwar ta ce MDD na fatan sauye-sauyen za su inganta rayuwar jama'a a fadin kasar.

An amince da shirin ne a makon da ya gabata, yayin wani taro da ya samu halarcin Firaminista Fayez Serraj da manyan jami'an majalisar koli ta kasar da na majalisar wakilai da na Babban Bankin kasar, da nufin farfado da tattalin arzikin kasar dake dakushewa.

Shirin ya kunshi sauya farashin musayar kudin kasar da na kasashen ketare, da sanya kudin da za a biya kan sayen takardar kudaden ketare da kuma magance matsalolin shirin tallafin man fetur na gwamnati. (Fa'iza Msutapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China