in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
MDD ta yi gargadi game da kai hari kan unguwannin jama'a a Libya
2018-09-21 11:13:50 cri
Yayin da bangarori masu adawa da juna ke ci gaba da gwabza fada a Libya, shirin wanzar da zaman lafiya na MDD a kasar (UNSMIL), ya yi gargadi game da kai hari unguwannin jama'a a Tripoli babban birnin kasar.

Cikin wata sanarwar gargadi da ya fitar, shirin ya tunatarwa bangarorin yarjejeniyar tsagaita bude wuta da suka cimma, da kuma haramcin da dokokin jin kai na kasa da kasa suka yi kan illata fararen hula.

Duk da yarjejeniyar tsagaita bude wuta da aka cimma karkashin MDD, ana ci gaba da gwabza fada a kudancin Tripoli tsakanin dakarun gwamnatin da MDD ke marawa baya da kuma biget ta 7 ta 'yan tawaye dake birnin Tarhua, mai nisan kilomita 80 daga kudu maso gabashin Tripli,.

Yarjejeniyar ta kawo karshen fadan da ya yi sanadin mutuwar mutane a kalla 78 tare da raunata wasu 210, galibinsu fararen hula, kafin kuma wani sabo ya barke kwanaki 4 da suka wuce. (Fa'iza Msutapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China