in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Trump zai bayyana shirin wanzar da zaman lafiya tsakanin Isra'ila da Palestinu nan da watanni 4
2018-09-27 10:58:54 cri
Shugaban kasar Amurka Donald Trump ya sanar a jiya Laraba cewa, zai gabatar da muhimmin shirin tabbatar da zaman lafiya tsakanin Isra'ila da Palestinu, ya kara da cewa yana bukatar kasashen biyu su warware sabanin dake tsakaninsu.

Da yake ganawa da firaiministan Isra'ila Benjamin Netanyahu a taron MDD, Trump ya ce yana sa ran shirin kawo zaman lafiya tsakanin Isra'ila da Palestinu zai kammala nan da watanni biyu ko uku zuwa wata hudu.

Gwamnatin Trump ta sha nanata cewa za ta goyi bayan dukkan bangarorin biyu idan har suka amince da shirin zaman lafiyar. Sai dai wannan ne karon farko da Trump ya fito fili ya goyi bayan wannan batu.

Sai dai kuma, Husam Zomlot, shugaban ofishin kungiyar fafutukar ceto al'ummar Palestinawa (PLO) dake Washington, ya shedawa kamfanin dillancin labarai na AFP cewa, kalaman na fadar White House sun sha banban da abin da take aiwatarwa a zahiri kuma al'amari ne a bayyane karara cewa matakan da Amurkar ke dauka suna kara lalata duk wani yunkuri na samun maslaha tsakanin kasashen biyu.

Ya kara da cewa, kalaman da Trump ya yi kadai ba za su wadatar ba wajen gamsar da al'ummar Palestinawa don su amince su hau teburin sulhu don tattaunawar zaman lafiyar. (Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China