in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Jami'in MDD ya bukaci a kara himma wajen kare hakkin dan adam
2018-09-27 10:02:02 cri
Babban magatakardan MDD Antonio Guterres a jiya Laraba ya bukaci a kara kaimi wajen kare hakkin bil adama a kasa da kasa saboda har yanzu akwai babban aiki da duniya ke bukatar aiwatarwa domin dan adam ya samu cikakken 'yanci na gaskiya.

Da yake jawabi a lokacin babban taron MDD karo na 70 game da batun kare hakkin dan adam, Guterres ya ce, mutane da yawa a fadin duniya har yanzu suna fama da matsalar cin zarafi na take musu hakki.

Ya ce banbancin jinsi yana daya daga cikin manyan kalubalolin da suka shafi hakkin dan adam, sai kuma batun 'yan gudun hijira da 'yan ci rani, sai mutanen da ba su kiyaye dokokin jinsi, da dukkan nau'ikan 'yan tsiraru, ana matukar take musu hakki da kuma cin zarafinsu.

Babban jami'in na MDD ya yi kira musamman ga matasa da su shiga a dama da su wajen yaki da take hakkin dan adam. (Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China