in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin na daukar nauyin babbar kasa wajen neman ci gaban duniya
2018-10-01 17:38:44 cri
"Yau ne Sinawa ke bikin cika shekaru 69 da kafa sabuwar kasar Sin. A safiyar wannan rana, na saki tattabara, don su kawo miki ganye na zaitun. Suna tafiya cikin tsaunuka, muna taya ki murnar kafa sabuwar kasar Sin, ina son kawar miki damuwa, ina fatan kina cikin zaman lafiya har abada…"

A ranar 1 ga watan Oktoban ko wace shekara, Sinawa su kan rera wannan waka mai taken "Yau ranar haihuwarki ce". Kuma kalmomin "tattabara" da "ganye na zaitun" da aka yi amfani da su cikin wannan waka, suna nufin kyakyyawan fatan al'ummomin kasa da kasa wajen neman zaman lafiya.

A yayin taron kolin dandalin tattaunawar hadin gwiwar Sin da Afirka da aka yi a farkon watan Satumba, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya bayyana cewa, babban taken zamanin yau shi ne kiyaye zaman lafiya da neman ci gaba, kuma su ne babban burinmu a halin yanzu, ya kamata kasashen duniya su dauki nauyi tare yadda ya kamata domin cimma wannan buri.

A halin yanzu, duniya na fuskantar manyan kalubale, a matsayinta na kasa mai kiyaye tsarin kasa da kasa, wadda take kuma dukufa wajen habaka hadin gwiwar dake tsakanin kasa da kasa, ra'ayin kasar Sin kan yadda za a samu ci gaban duniya da kuma kiyaye zaman lafiyar kasa da kasa yana janyo hankulan gamayyar kasa da kasa kwarai da gaske.

An lura da cewa, a kokarin da ake na ganin an wanzar da zaman lafiya a duniya, kasar Sin, yayin da take kokarin raya tattalin arziki da inganta al'umma a gidanta, ta zama mai taka muhimmiyar rawa cikin ayyukan wanzar da zaman lafiya a duniya da MDD ke jagoranta. A cikin wasu kwanaki 3 da suka wuce, karin wasu jami'an kiyaye zaman lafiya na kasar Sin 100 sun tafi kasar Congo Kinshasa don fara gudanar da aikinsu a can. A cikin shekaru 28 da suka wuce, kasar Sin ta tura sojoji da 'yan sandan kasar da yawansu ya kai dubu 37 zuwa kasashe daban daban na duniya domin gudanar da aikin kiyaye zaman lafiya karkashin jagorancin MDD. Cikinsu har da wasu 21 da suka rasa rayukansu yayin wannan aiki. Yanzu kasar Sin ita ce kasa ta biyu a duniya dake samar da mafi yawan kudi don tallafawa ayyukan kiyaye zaman lafiya na MDD. Kana cikin kasashe 5 da ke da kujerun din-din-din a kwamitin sulhu na MDD, kasar Sin ita ce wadda ta tura jami'an kiyaye zaman lafiya mafi yawa.

A ganin Nick Birnback, mai magana da yawun sashin kula da aikin wanzar da zaman lafiya a duniya na MDD, a matsayinta na kasar dake da kujera din-din-din a kwamitin sulhu na MDD, kasar Sin ta kasance abin koyi ga sauran kasashen duniya, domin har yanzu wasu mambobin MDD ba sa son taimakawa yunkurin majalisar na wanzar da zaman lafiya. A cewar, mista Birnback, jefa kuri'a a MDD da samar da kudin da ake bukata dukkansu na da muhimmanci, amma taimakon da kasar Sin ta samar wa MDD na tura jami'an kiyaye zaman lafiya zuwa wuraren da ake fama da rikici shi ne mafi muhimmanci.

Kasar Sin kasa ne dake kan hanyar tasowa mafi girma a duniya, don haka ta fahimci radadin talauci, da wahalhalun da wata kasa, ko yanki, ko kuma wani iyali suke sha, yayin da suke fama da fatara. Bayan da kasar ta kwashe shekaru 40 tana kokarin gudanar da manufar yin gyare-gyare a gida da bude kofa ga kasashen waje, ta samu damar fitar da jama'arta kimanin miliyan 800 daga kangin talauci, har ma ta zama kasa ta biyu mafi karfin tattalin arziki a duniya. Duk da haka, har yanzu akwai mutane fiye da miliyan 30 dake fama da talauci a kasar, kana ma'aunin tattalin arziki na GDP na kasar yana matsayi na 71 a duniya. Don daidaita wannan yanayin da ake ciki, kasar Sin tana karfafa sassan kasar daban daban gwiwa domin su shiga a dama da su a aikin kau da talauci na shekaru 3, tare da burin sanya daukacin al'ummar kasar samun walwala nan da karshen shekarar 2020. Ban da haka, kasar ta yi kokarin yada ra'ayinta na kafa "al'umma mai kyakkyawar makomar bai daya" a duniya, tare da samar da dimbin gudunmawa a wannan fanni. Kasar Sin ta kuma tsaya kan manufar "tattaunawa, da bunkasuwa tare, da kuma samun moriya tare", a yayin da take hadin gwiwa da sauran kasashe karkashin shawawar "Ziri daya da Hanya daya", kana tana raba wa sauran kasashe fasahohi da damammaki da ta samu domin dukkan kasashen su samu damar samun ci gaba tare.

Sabuwar kididdigar da aka fitar na nuna cewa, bayan da kasar Sin ta kaddamar da shawarar "Ziri daya da Hanya daya" a shekarar 2013, yawan kasashen duniya da kungiyoyin kasa da kasa wadanda suka kulla yarjejeniyar hadin gwiwa da kasar Sin ya kai fiye da dari 1. Sannan yawan darajar kayayyakin ciniki tsakanin kasar Sin da kasashen dake cikin shawarar ya kai dalar Amurka biliyan dubu 5, kana yawan jarin da aka zuba a yankunan raya tattalin arziki da cinikayya da kamfanonin kasar Sin suka kafa a wadannan kasashe ya kai dalar Amurka biliyan 28.9, inda aka samar da guraban aikin yi dubu 244, da kuma kudaden shiga kimanin dalar Amurka dubu 200 ko fiye.

Wannan sakamako ya kasance tamkar kyakkwar amsa ga shakkun da ake yi kan shawarar. Antonio Guterres, babban sakataren MDD ya yaba wa kasar Sin da ta more ci gaban da ta samu da kasashen Afirka ta hanyar kaddamar da shawarar "ziri daya da hanya daya". Sannan shugaban kasar Kenya Uhuru Kenyatta ya bayyana cewa, shawarar "Ziri daya da Hanya daya" tana da kyakkyawar makoma, sabo da kasashen da za su mayar da martani ga shawarar za su iya samun moriya da nasara tare, shi ne dalilin da ya sa kasar Kenya, da ma dukkan kasashen Afirka suke son karfafa hadin gwiwa tsakaninsu da kasar Sin.

A kowace shekara, ana bikin murnar ranar kafuwar sabuwar kasar Sin. A yayin da Sinawa ke murnar wannan rana a bana, hukumar birnin San Francisco ta kasar Amurka ta kebe ranar 1 ga watan Oktoba ta zama "Ranar raya da al'adu da sada zumunta tsakanin Sin da Amurka", domin bayyana yadda birnin yake da imani da niyya wajen kara bunkasa hadin gwiwar moriyar juna irin ta sada zumunta tsakaninsa da kasar Sin.

A lokacin da tarihi da kuma zamaninmu suke samun ci gaba, babu wata kasa da za ta iya zama ita kawai. Yayin da ta kasance wata kasa mai tasowa mafi girma a duniya wadda ta fi saurin samun ci gaba da kuma bude kofarta ga sauran kasashen duniya, tabbas za a gano cewa, kasar Sin za ta nuna sabon kwazo da himma da kuma ba da sabuwar gudummawa wajen tabbatar da zaman lafiya da bunkasuwar duniya baki daya kamar yadda ta saba yi a kullum. (Marubuciya: Guan Juanjuan; Masu Fassarawa: Sanusi Chen, Bello Wang, Maryam Yang, dukkansu ma'aikatan CRI)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China