in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sharhi: Yakin ciniki ba zai taimaka wajen warware matsalolin da ake fuskanta ba
2018-09-18 19:09:30 cri
A jiya Litinin, kasar Amurka ta sanar da cewa, za ta karbi karin harajin kwastam na kashi 10% kan wasu kayayyakin da darajarsu ta kai dala biliyan 200, wadanda kasar Sin za ta shigar kasar, manufar da za ta fara aiki a ranar 24 ga watan da muke ciki. Ban da haka, kasar ta yi barazanar daukar karin matakai masu alaka da harajin kwastam a nan gaba. Dangane da batun, kakakin ma'aikatar kasuwancin kasar Sin ya ce, kasarsa ta bayyana rashin jin dadin ta game da manufar, sa'an nan don kare hakkinta, da tsarin ciniki cikin 'yanci na duniya, Sin za ta dauki makamancin wannan mataki, kan kayayyakin da kasar Amurka za ta shigo da su kasarta.

Rashin sanin ya kamata da kasar Amurka ta nuna, ya kara tsaurara yanayin da kasashen Sin da Amurka suke ciki na yakin ciniki. Hakika, a wasu kwanakin da suka wuce, kasar Amurka ta nuna bukatarta ta yin shawarwari da kasar Sin, kan batun tattalin arziki da cinikayya, lamarin da ya faranta wa kasar Sin ranta, har ma yanayin tattalin arzikin duniya ya dan farfado sakamakon lamarin. Amma yanzu, ba zato ba tsammani, kasar Amurka ta sanar da karbar karin harajin kwastam kan kayayyakin Sin. Nufinta shi ne kara matsawa kasar Sin lamba, don neman sanya kasar Sin ta nuna ra'ayin sassauci.

Dangane da matakin da Amurka ta dauka, gwamnatin kasar Sin ta ce, wannan lamarin ya dora wani yanayi na rashin tabbas kan shawarwarin da ake yi tsakanin bangarorin 2. Saboda haka kasar Sin na fatan ganin kasar Amurka ta lura da mummunan sakamakon da batun zai iya haddasawa, da daidaita kuskurenta cikin lokaci.

Hakika duk wani matakin da Amurka ta dauka, kasar Sin tana da isashen karfi na kula da harkokin kanta, da kare moriyarta da ta al'ummarta, gami da ba da kariya ga tsarin ciniki cikin 'yanci, da wanda ya shafi bangarori daban daban.

Yanzu haka idan mun yi nazari kan kayayyakin kasar Sin da kasar Amurka za ta kara karbar haraji a kansu, za a gano cewa, da yawa daga cikinsu ba su da alaka da jama'ar kasar Sin, amma suna shafar zaman rayuwar jama'ar kasar Amurka. A halin yanzu lokacin sayen kayayyaki don share fagen bikin Kirsimeti na karatowa, wannan yanayi ya sa wasu kafofin watsa labaru na kasar Amurka suka nuna damuwa cewa, matakin kara harajin da gwamnatin kasar ta dauka, ka iya haifar da mummunan tasiri ga zaman rayuwar jama'ar kasar Amurka matuka. Ganin wannan ya sa wasu kungiyoyin sana'o'i da na jama'ar kasar Amurka, gami da kwararrun masanan ilimin cinikayya, suka nuna kin amincewa ga manufar da gwamnatin kasar ta dauka, na kara harajin kwastam da take karbar. A nashi bangare, Adam Posen, shugaban cibiyar nazarin tattalin arzikin kasa da kasa ta Peterson na kasar Amurka, ya ce, manufar karbar karin harajin da gwamnatin Trump ta dauka ba za ta yi amfani ba.

Sa'an nan kuma, a farkon watan Agusta, kasar Sin ta tsai da kudurin kara haraji kan hajojin kasar Amurka masu darajar dallar Amurka biliyan 60, domin rage tasirin da takaddamar cinikin dake tsakanin Sin da Amurka ta yiwa al'ummomi da kamfanonin kasar Sin. A sa'i daya kuma, kasar Sin za ta ci gaba da mai da martani ga kasar Amurka, bisa matakan da za ta dauka a nan gaba. Ma'anar ita ce, kome matakan da kasar Amurka za ta dauka, kasar Sin za ta iya fuskantar su yadda ya kamata.

Na uku, tun daga farkon shekarar bana, kasar Sin ta ci gaba da rage dogaron ta kan kasashen ketare domin neman bunkasuwar tattalin arziki, musamman ma kan kasar Amurka. Lamarin da ya nuna mana cewa, bunkasuwar tattalin arziki na kasar Sin, ta fi dogaro kan harkokin zuba jari da kuma saya da sayarwa a cikin kasa. A sa'i daya kuma, manyan kasuwannin dake kunshe da mutane kimanin biliyan 1.4 na kasar Sin, bunkasuwar harkokin masana'antu na iri daban daban, da kuma tsarin bude kofa ga waje na kasar Sin, da dai sauran makamantansu, suna goyawa kasar baya, wajen aiwatar da harkokinta yadda ya kamata, da kuma fuskantar matsalolin da kasashen ketare suka haifar mata.

Donald Trump ya ce, a matsayin sa na shugaban kasar Amurka, kare moriyar ma'aikata, manoma, makiyaya, kamfanoni da kuma kasarsa shi ne babban burinsa. Idan da gaske yake, to ya kamata ya duba wasikar kin takaddamar ciniki da kungiyoyin masu sana'o'i daban daban har guda 150 suka aika masa, ya kuma saurari kiran da kungiyoyi sama da 80 suka yi cewar, kara haraji zai kawo illa ga kasar Amurka. Tushen cinikin dake tsakanin Sin da Amurka shi ne yin hadin gwiwa domin cimma moriyar juna, shi ya sa, yin hadin gwiwar shi ne hanya madaidaiciya kadai ga kasashen biyu. Idan Donald Trump yana son kiyaye moriyar kasar Amurka da ta al'ummominsa, ya kamata ya gyara kuskuren da ya yi cikin sauri, ya kuma nuna gaskiyarsa wajen yin shawarwari da bangaren Sin, domin warware matsalar takaddamar cinikin dake tsakanin kasashen biyu. (Bello/Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China