in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An kafa tashar mashigin teku mai sarrafa kanta a birnin Shanghai
2018-09-18 14:21:16 cri

An kafa tashar mashigin teku ta Yangshan a birnin Shanghai, wadda ita ce tashar farko da aka gina a wani karamin tsibiri a kasar Sin. An kafa tashar mashigin tekun wadda ke iya sarrafa kanta kuma ita ce tasha mai sarrafa kanta mafi girma a duniya.

Tasha ta hudu ta mashigin tekun Yangshan dake kudu maso gabashin birnin Shanghai, tasha ce mafi girma mai sarrafa kanta a duniya, kana fasahohin sarrafarta ta zama matsayin koli a duniya. Ana ajiye manyan akwatuna da dama a wurin. Motoci masu sarrafa kansu suna yin jigilar kayayyaki bi da bi ne.

Babban direktan sashen bada jagoranci ga aikin gina tasha ta hudu ta mashigin tekun Yangshan Zhang Bin ya bayyanawa 'yan jarida cewa, ana gano wurin da motoci masu sarrafa kansu suke tafiya bisa kusa mai karfin maganadiso, kuma ana iya canja hanyar tafiyarsu idan motoci biyu suna kusa har na nisa kasa da mita daya. Masu kula da na'urorin suna sarrafa motocin daga inji daga abubuwa masu nauyi da hanyoyin tafiyar motoci. Domin aka samu irin na'urori na zamani, an fi tasoshin mashigin teku na gargajiya a fannoni daban daban. Zhang Bin ya bayyana cewa,

"Tsarin sarrafa na'urori da kansu yana iya taimakawa wajen gudanar da ayyukan tashar mashigin teku yadda ya kamata. Wannan yana da babbar ma'ana ga inganta karfin gudanar da aikin a tashar, mai yiwuwa ne za a zarce tasoshin mashigin teku na gargajiya a sakamakon amfani da tsarin."

Motocin yin jigilar kaya masu sarrafa kansu wadanda kamfanin masana'antun samar da manyan injuna na Zhenhua na birnin Shanghai suka nazari kera su, su ne muhimmin kashi na tsarin sarrafa na'urori da kansu a tasha ta hudu ta mashigin tekun Yangshan. Ta wannan tsari, ana iya dagawa da sauke manyan akwatuna da yin jigilarsu da ajiye su ta na'urori masu sarrafa kansu. Shugaba mai kula da fasahohin tsarin sarrafa na'urorin na aikin gina tasha ta hudu ta mashigin tekun Yangshan Yu Jun ya bayyana cewa,

"Wannan ne tsarin sarrafa motoci masu sarrafa kansu da muke fi yin amfani da shi a halin yanzu, yawan na'urorin da ake yin amfani da tsarin ya kai fiye da 130. Don hakan, mun cimma burin kasancewa a matsayin gaba a wannan fanni."

Tashar mashigin teku mai sarrafa kanta ta kyautata yanayin gudanar da ayyuka na ma'aikatan dake aikin a nan kai tsaye, da rage yawan kudin da aka kashe a wannan fanni. Dalilin da ya sa aka samu nasarar shi ne ana samun fasahohin zamani da kuma tsara ayyukan da shugabanni da masu kula da aikin suka yi a wannan fanni. Sakataren kwamitin jam'iyyar kwaminis ta Sin kuma shugaban kamfanin harkokin tasoshin mashigin teku na birnin Shanghai Chen Xuyuan ya bayyana cewa,

"Mun tsara burin gina tasoshin mashigin teku na zamani da kiyaye muhalli da kimiyya da fasaha da kuma gudanar da ayyuka yadda ya kamata. A fannin fasahohin zamani, muna kokarin raya fasahohin sadarwa da kimiyya, tasha ta hudu ta mashigin tekun Yangshan ita ce misali mai kyau a wannan fanni. A fannin kimiyya da fasaha, an kafa cibiyar kimiyya da fasaha ta tasoshin mashin teku ta kasar don aiwatar da aikin raya tasohin mashigin teku masu kimiyya da fasaha na shekaru 3. Kana a raya tasoshin mashigin teku ba tare da gurbata muhalli ba. A cikin shekaru 40 da suka gabata ana kokarin raya tasoshin mashigin teku na birnin Shanghai, musamman shekaru 10 da suka gabata, an samu nasarori da dama, yawan makamashin da ake amfani da su a tasohin mashigin teku ya ragu da kashi 5 cikin dari a kowace shekara. Kana ana kokarin raya ingancin ayyuka na tasoshin mashigin teku, yawan manyan akwatunan da ake yin jigila a kowane mita 100 na layin mashigin teku ya kai dubu 290, wanda ya zarce sauran tasoshin mashigin teku na duniya." (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China