in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
WHO: Shugabannin duniya sun sha alwashin kakkabe cutar tarin fuka daga doron duniya
2018-09-27 09:49:58 cri
Hukumar lafiya ta duniya WHO, ta ce shugabannin kasa da kasa dake halartar taron kolin MDD, sun sha alwashin daukar karin matakai don ganin an shawo kan cutar tarin fuka nan da shekarar 2022.

WHO ta ce shugabannin sun amince da kudurin samar da jinya ga mutane kimanin miliyan 40, dake dauke da wannan cuta nan da shekarar ta 2022. Kaza lika za su samar wa mutane miliyan 30, da dama ta kandagarki daga kamuwa da ita.

Wannan ne dai karon farko da jagororin kasashen duniya suka gudanar da taron koli game da yaki da cutar tarin fuka, a kuma taron na ranar Laraba wanda ya gudana a helkwatar MDD dake birnin New York, an amince da tara kudi da yawan su ya kai dalar Amurka biliyan 13 a duk shekara nan da shekarar 2022, don gudanar da kandagarki, da kuma wasu karin dala biliyan 2 don gudanar da bincike.

Har ila yau WHO ta ce za a dauki kwararan matakai, na shawo kan kalubalen da nau'in cutar mai bijirewa magani ke haifarwa, kana za a samar da matakai na kau da nuna kyama ga masu dauke da cutar tarin fuka a sassan duniya daban daban. Shugabannin dai sun amince cewa nasarar da ake samu a yanzu haka, ta yi kasa da bukatar da ake da ita game da kakkabe wannan cuta.

Ya zuwa yanzu cutar tarin fuka na sahun gaba wajen hallaka jama'a, inda alkaluma ke nuna cewa a shekarar 2017, cutar ta sabbaba rasuwar mutane miliyan 1.6, ciki hadda mutane 300,000 dake dauke da cutar HIV/AIDs ko SIDA. Baya ga wasu mutanen kimanin miliyan 10 da cutar ta tarin fuka ta kwantar. (Saminu Hassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China