in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
MDD ta baiwa rukunin sojin sama mai saukar ungulu na kasar Sin mai aikin kiyaye zaman lafiya lambar yabo
2018-07-16 10:21:44 cri

MDD ta baiwa rukuni na farko, na jiragen sama masu saukar ungulu na kasar Sin dake aikin kiyaye zaman lafiya lambar yabo madaukakiya ta zaman lafiya a jiya Lahadi 15 ga watan nan, a sansanin Al-Fashir na yankin Darfur dake kasar Sudan. An dai baiwa daukacin mambobin rukunin sojoji su 140 wannan lamba ta yabo.

Da sanyin safiyar wannan rana kuma, wakilin musamman na tawagar musamman ta MDD da AU dake aiki a Darfur (UNAMID) Jeremiah Mamabolo, ya duba faretin rukunin, karkashin rakiyar shugaban rukunin Chen Wenlong. A gun bikin gabatar da lambar yabon, Mista Mamabolo ya ce, rukunin ya gudanar da aiki mai kyau a fannin sa kaimi, ga farfado da yankin Darfur, da samar da tallafin jin kai, ta yadda ayyukan sa suka kai matsayin koyi a ayyukan tawagar UNAMID. (Amina Xu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China