A wani yunkuri da daukacin mambobin kwamitin suka amince da shi, kwamitin ya sabunta aikin shirin UNAMID a Dafur, wanda na hadin gwiwa ne tsakanin Tarayyar Afrika da MDD.
Kudurin ya kuma bukaci shirin ya ci gaba da daukan mataki kan duk wani abu dake masa barazana ko wadanda yake karewa.
Kwamitin MDD ne ya kafa UNAMID mai hedkwata a El Fasher na arewacin Dafur a ranar 31 ga watan Yulin 2007, bayan amincewa da kuduri mai lamba 1769.
Ayyukansa ya kunshi kare fararen hula da taimakawa wajen kai agajin jin kai da shiga tsakanin gwamnati da 'yan adawa da kuma warware rikici tsakanin al'ummomi. (Fa'iza Mustapha)