Wang Yi ya ce ko da a baya, kasar Sin ba ta taba tsoma baki a harkokin cikin gidan wata kasa ba, ba kuma za ta yi hakan a yanzu ko a nan gaba ba.
Ministan ya ce kauracewa shiga sharo ba shanu, al'ada ce ta gargajiya da aka san Sin a kai, take kuma samun yabo bisa riko da ita, ba kuma za ta sauya daga wannan matsaya ba.
Daga nan sai ya yi kira ga kasashen duniya, da su yi riko da wannan ka'ida ta MDD, wadda ta haramta daukar duk wani mataki, na tsoma baki a harkokin sauran kasashe na daban. (Saminu Hassan)