Moon Jae-in ya bayyana a wannan rana cewa, shi da Kim Jong-un sun yi ganawa a kwanakin baya, kuma ya yi imani Kim Jong-un zai sa kaimi ga kawar da makaman nukiliya a zirin Koriya. Idan kasar Amurka ta dauki matakai masu dacewa da yin imani da juna, bangarori daban daban da abin ya shafa za su gaggauta aikin kawar da makaman nukiliya a zirin Koriya. Ya yi imani cewa, za a cimma burin kawar da makaman nukiliya a zirin Koriya a lokacin wa'adin Trump. Kana ya ce, kasar Amurka ta yi alkawarin dakatar da nuna kiyayya ga kasar Koriya ta Arewa, tare da yin kokarin raya dangantaka dake tsakanin kasashen biyu. (Zainab)