in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Asibitoci a Gaza na daf da dakatar da aiki sakamakon karancin makamashi
2018-09-10 10:53:20 cri
Kakakin ma'aikatar lafiya a zirin Gaza Ashraf al-Qedra, ya yi gargadin cewa, mai yiwuwa ne wasu asibitocin yankin su dakatar da ayyukan su, sakamakon karancin wutar lantarki, da man fetur da ake amfani da shi, wajen tada injunan samar da wuta. Mr. Al-Qedra ya bayyana hakan ne cikin sanarwa da ya fitar.

Shi ma daraktan babban asibitin Beit Hanoun dake arewacin zirin Gaza Jamil Suleiman, ya ce karancin makamashin na barazana ga ayyukan aibitin da yake jagoranta. Yana mai cewa kimanin mutane 350,000 ne ke fuskantar matsaloli na kula da lafiya sakamakon wannan kalubalen.

Sulaiman wanda ke wannan tsokaci, yayin wani taron ganawa da manema labarai ya kara da cewa, matsalar da ake fuskanta ta tilasawa asibitoci, amfani da kananan injunan samar da wutar lantarki, da rage yawan mai da ake konawa a kullum. Ya ce hakan ya kuma tilasawa asibitoci jinkirta ayyukan tiyata ga marasa lafiya, da jinkiri wajen yin gwaje gwajen jini, da na daukar hoton kirgi, har ma da hidimomi na sashen tsaftace tufafi da muhalli a asibitin.

A ranar Larabar da ta gabata, MDD ta ayyana bukatar samar da tallafi, domin gudamar da muhimman ayyuka a Gaza, duba da yadda kayakkakin bukatu suka riga suka kare a zirin. (Saminu)
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China