Abbas yayi wannan tsokaci ne a lokacin ganawa da wata tawagar da ke wakiltar tsoffin mambobi masu tsattsauran ra'ayi na majalisar kasar Israeli, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na WAFA ya ambata.
Abbas ya duba irin cigaban siyasa na baya bayan nan da aka samu, da kuma irin mummunan halin da ake ciki a sanadiyyar matakan da Israila ke dauka da kuma irin goyon bayan da take samu daga gwamnatin Amurka, inji WAFA.
Tun da farko a wannan rana, wakilin musamman na MDD kan batun zaman lafiyar yankin gabas ta tsakiya Nickolay Mladenov, ya gargadi Israel dangane da rusa kauyen Al Khan Al-Ahmar Bedouin dake gabashin birnin kudus.
A wata sanarwa da aka aike wa kamfanin dillancin labarai na Xinhua, Mladenov, ya bukaci hukumomin Isra'ila da kada su cigaba da rusa matsugunan al'ummar Palastinawa a yammacin kogin Jordan.