in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Wasu 'yan kasar Uganda sun tsallake gwajin cutar Ebola
2018-08-16 09:40:58 cri

Hukumar lafiya ta duniya WHO ta tabbatar da cewa, wasu 'yan kasar Uganda su 3 da aka yiwa gwajin cutar Ebola ba sa dauke da cutar.

WHO ta ce, gwajin da aka yiwa mutane 2 daga cikin 3, wadanda aka samu a gundumar Kasese dake kan iyakar kasar da janhuriyar dimokaradiyyar Congo ya nuna mutane ba su kamu da cutar ba. Kana ta ukun su wadda mace ce mai juna biyu, wadda ta rasu a asibitin Kaganda dake gundumar Kasese, ita ma an gano cewa, ba Ebola ce ta hallaka ta ba.

An dai gudanar da gwajin kwayoyin halittun mutanen 3 ne a cibiyar bincike dake wajen birnin Kampala.

Da yake karin haske game da hakan, wakilin hukumar ta WHO a Uganda Yonas Tegegn Woldemariam, ya bayyana wa kamfanin dillancin labarai na Xinhua cewa, ba wata barazana ta yaduwar Ebola a kasar Uganda.

Game da matakan da suka dace a dauka domin dakile fadadar cutar kuwa, Mr. Woldemariam ya ce, Uganda da janhuriyar dimokaradiyyar Congo na da iyakoki a bude da al'ummar su ke zirga zirga cikin su babu wani kaidi, don haka ya dace a rika tantance yanayin lafiyar mutanen dake shige da fice ta kan iyakokin. Kaza lika akwai bukatar horas da jami'an lafiya game da hanyoyin daukar matakan gaggawa, na dakile yaduwar cutar ba tare da wani jinkiri ba.(Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China