in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin ta bayyana matukar rashin amincewarta da aniyar Amurka ta sayarwa Taiwan makamai
2018-09-26 09:56:37 cri
Kakakin ma'aikatar tsaron kasar Sin Ren Guoqiang, ya ce kasar sa na matukar Allah wadai, da aniyar Amurka ta sayarwa yankin Taiwan makamai. Ren Guoqiang, ya ce Sin ta shirya zantawa da tsagin Amurka domin shawo kan wannan kalubale.

Ya ce "Taiwan yanki ne na kasar Sin, kuma sayar mata da makamai ya sabawa manufar nan ta wanzuwar kasar Sin daya tak a duniya, da ma tushen kawancen dake tsakanin ta da Amurka".

Kaza lika jami'in ya ce batun zai kasance wani mataki na karan tsaye ga dokokin da Sin da Amurka suka amincewa, kana tsoma hannu ne cikin harkokin cikin gidan Sin, lamarin da zai haifar da illa ga sha'anin tsaron kasar Sin, da kawancen dake tsakanin dakarun sojojin sassan biyu, da ma yanayin zaman lafiya da tsaro a zirin Taiwan.

A don haka kakakin ma'aikatar tsaron Sin ya ce rundunar sojin Sin, a shirye take ta dauki dukkanin matakan da suka dace, domin kare 'yancin kai na yankunan Sin. A hannu guda kuma, Sin na fatan Amurka za ta mutunta kudurin nan na wanzuwar kasar Sin daya tak a duniya, ta dakatar da kwangilar sayarwa Taiwan makamai, wanda hakan zai kare darajar kawancen dake tsakanin sassan biyu.

Kalaman jami'in na Sin dai na zuwa ne bayan da gwamnatin Amurka ta gabatarwa majalissar dokokin kasar, wani kuduri na neman amincewa ta sayarwa yankin Taiwan wasu makamai, na kimanin dalar Amurka miliyan 330.(Saminu Alhassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China