Jami'in wanda ya sanar da hakan yayin taron maname labarai yau Talata a nan birnin Beijing, ya ce, shirin Amurka na sayarwa yakin na Taiwan makamai ya sabawa muradun dokoki da alakar kasa da kasa, da ma manufar kasar Sin daya tak a duniya da sanarwar guda uku da Sin da Amurka suka sanyawa hannu. Kuma wannan yana iya yiwa muradun tsaro da 'yancin kasar Sin illa nesa ba kusa ba.(Ibrahim)