Mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Lu Kang wanda ya bayyana hakan yau yayin taron maname labarai, ya ce matakin da majalisar WHA ta dauka ya dada kare martaba da kimar kudurorin babban taron MDD da ma na majalisar harkokin kiwon lafiya, kuma hakan ya nuna cewa, duniya ta amince da manufar kasar Sin daya tak a duniya kuma ya yi daidai da yanayin da ake ciki a halin yanzu.
Jami'in na kasar Sin ya kara da cewa, gwamnatin kasar Sin za ta nazarci batun halartar yankin na Taiwan cikin harkokin kasa da kasa bisa manufar kasar Sin daya tak a duniya.(Ibrahim)