Wata sanarwa da ma'aikatar ta rabawa manema labarai ta ce, gwamnatin Burkina-Fason ta dauki wannan mataki ne a yau. Shugaban kasar Faso Marc Christian Kabore ya umarci ma'aikatar harkokin wajen da hadin gwiwa ta kasar, da ta kammala dukkan shirye-shiryen da suka wajaba na rufe ofishin jakadancin kasar dake Taipei da ma na Taiwan dake kasar. (Ibrahim)