in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Sin ta jaddada martaba manufar kasar daya tak a duniya a matsayin sharadi na shigar yankin Taiwan harkokin kasa da kasa
2017-12-25 20:25:37 cri

Mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Hua Chunying ta sake jaddada cewa, idan har yankin Taiwan yana son shiga a dama da shi a harkokin kasa da kasa wajibi ne ya martaba manufar kasar Sin daya tak a duniya.

Madam Hua ta bayyana hakan ne yayin da take mayar ba da amsa kan tambayar da aka yi mata game da kalaman da ministan harkokin wajen kasar Sweden Margot Wallstom, ya yi kan shigar yankin Taiwan na kasar Sin cikin kungiyoyin kasa da kasa.

Hua ta ce, game da batun shigar yankin Taiwan cikin kungiyoyin kasa da kasa, har kullum kasar Sin tana bayyanawa karara cewa, ya kamata hakan ya kasance karkashin manufar kasar Sin daya tak a duniya.

Jami'ar ta kuma nanata cewa, batun yankin Taiwan, batu ne da ya shafi harkokin cikin gidan kasar Sin, don haka kasar Sin tana adawa da yadda wasu kasashe ke kalaman da ba su dace ba kan batun.(Ibrahim Yaya)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China