in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin: Firaminista Li Keqiang ya yi bayani kan manufofi masu alaka da tattalin arziki na kasar Sin
2018-09-21 18:46:15 cri
A jiya Alhamis, an kammala taron dandalin Davos a birnin Tianjin na kasar Sin. Sa'an nan a yau, kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Geng Shuang, ya bayyana cewa, cikin jawabin da firaministan kasar Li Keqiang ya yi a wajen taron, ya yi kira da a kara kokarin kirkiro sabbin fasahohi, a bangaren masana'antu, don sa kaimi ga cigaban tattalin arzikin duniya.

Ban da haka kuma, ta jawabin firaminista Li, za a iya sanin wasu abubuwa 3, wadanda suka hada da, na farko, kasar Sin tana kokarin kare tsarin dunkulewar tattalin arzikin duniya waje guda; na biyu, tattalin arzikin na samun cigaba; da kuma na 3, kasar Sin za ta tsaya kan manufarta ta yin gyare-gyare a gida da bude kofa ga kasashen waje. (Bello Wang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China