in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugabannin Rasha da Koriya ta Kudu sun jaddada muhimmancin raba zirin Koriya da makaman nukiliya
2018-06-23 15:50:37 cri

Shugaban Rasha Vladimir Putin da takwaransa na Koriya ta Kudu Moon Jae-in, sun gana a jiya Juma'a, inda suka fitar da wata hadaddiyar sanarwa, da ta jaddada niyyar kasashen biyu na ci gaba da kokari domin cimma burin raba zirin Koriya da makaman nukiliya.

Yayin ganawar ta su, Putin ya bayyana cewa, har kullum Rasha tana kokarin daidaita batun zirin Koriya. Inda a nasa bangaren, Moon Jae-in ya bayyana cewa, kasashen biyu sun cimma matsaya guda tare da hadin gwiwa game da raba zirin Koriya da makaman nukiliya da tabbatar da zaman lafiya a zirin.

Labarin da aka wallafa a shafin yanar gizo na shugaban Rasha na cewa, cikin sanarwar hadin gwiwa da suka fitar, shugabannin biyu sun yaba da sakamakon da shugabannin kasashen Amurka da Koriya ta Arewa suka samu yayin ganawarsu a kasar Singapore, kuma suna fatan yarjejeniyar da sassan biyu suka daddale za ta taka rawa wajen tabbatar da kwanciyar hankali a zirin Koriya, tare kuma da cimma burin raba zirin da makaman nukiliya.

Moon Jae-in ya isa birnin Moscow na Rasha ne a ranar 19 ga watan nan, domin ziyarar aiki ta kwanaki uku a kasar. Kuma wannan ne karo na farko da shugaban Koriya ta Kudu mai ci ya kai ziyara Rasha cikin shekaru 19 da suka gabata.(Jamila)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China