in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Amurka za ta dakatar da atisayen soji tsakaninta da Koriya ta Kudu
2018-06-23 16:08:07 cri

Kakakin ma'aikatar tsaron Amurka ya sanar a jiya cewa, domin tabbatar da sakamakon da aka samu yayin ganawar shugabannin kasashen Amurka da Koriya ta Arewa a kasar Singapore ranar 12 ga wata, gwamnatin kasarsa za ta dakatar da wasu atisayen soji da ake yi tsakaninta da Koriya ta Kudu.

A baya ma'aikatar tsaron Amurka ta bayyana cewa, atisayen sojin dake gudana cikin hadin gwiwa tsakaninta da Koriya ta Kudu, na kariya ne, Amma a ranar 12 ga wata, bayan ganarwar shugaban Amurka Donald Trump da shugaban Koriya ta Arewa, Trump ya ce zai dakatar da atisayen, wanda ya bayyana a matsayin mai "kawo barazana" da lakume kudi da yawa, muddin dai Amurka da Koriya ta Arewar suka ci gaba da gudanar da sahihan shawarwari a tsakaninsu.(Jamila)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China