Fadar White House ta Amurka, ta ce shugaban kasar Donald Trump, da takwaransa na Koriya ta arewa Kim Jong Un, za su gana ne a Otel din Capella dake tsibirin Sentosa na Singapore.
Kakakin fadar White House Sarah Sanders ce ta wallafa bayanan inda shugabannin za su gana jiya a shafinta na Twitter.
Ta kara da cewa suna godiya ga al'ummar Singapore masu masaukin baki.
A jiyan ne kuma Shugaba Trump din ya ce yana fatan ganawarsa da Shugaba Kim, zai bude babin fara wani muhimmin batu. (Fa'iza Mustapha)