in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Palasdinu ta yanke shawarar farfado da gwamnatinta dake gabashin birnin Kudus
2018-05-09 10:45:48 cri

Mamban kwamitin gudanarwa, na kungiyar 'yantar da Palasdinawa PLO Ahmad Majdalani, ya bayyana a jiya cewa, shugabannin Palasdinu sun yanke shawarar sake bude gwamnatinsu dake gabashin birnin Kudus, wadda Isra'ila ta tarwatsa a shekarar 1967, a wani mataki na mayar da martani ga matakin da Amurka ta dauka, na mayar da ofishin jakadancinta birnin Kudus daga Tel Aviv. Sai dai jami'in bai bayyana hakikanin lokacin farfado da gwamnatin ba tukuna.

Har ila yau, Ahmad Majdalani, ya shedawa manema labarai cewa, mayar da ofishin jakadancinta zuwa birnin Kudus da Amurka ta yi, na nufin kalubalantar niyyar kasashen duniya na samar da zaman lafiya da dokar kasa da kasa, har da ma tunzura zukatan Palasdinawa, Larabawa, Musulmai da mabiya addinin Kirista. A don haka, shugabannin Palasdinu za su mai da karin martani kan Amurka, ta hanyar neman shiga karin kungiyoyin kasa da kasa da sauran wasu matakai. (Amina Xu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China