A yayin wani taron manema labarai da aka yi a wannan rana, Gong Xiaosheng ya ce, babban burin ziyarar tasa a wannan karo a Palasdinu, Isra'ila da Masar shi ne yin musanyar ra'ayi da bangarori masu ruwa da tsaki kan halin dake kara tsananta tsakanin Palasdinu da Isra'ila da dai sauran manyan matsaloli a wannan yanki.
Bangarori mahalarta taro su ma sun yi maraba da sabuwar gudunmawa da Sin take bayarwa wajen wanzar da zaman lafiya a yankin.
Gong Xiaosheng ya ce, Sin na nacewa ga warware rikicin banganrorin biyu ta hanyar yin shawarwari cikin lumana, kuma Sin na fatan kara ba da gudunmawa na ganin an wanzar da zaman lafiya a yankin, don kwantar da hankali da tabbatar da zaman lafiya a yankin.
Kasar Sin na ganin cewa, ya kamata kasashen duniya su nace ga manufar kafa kasashe biyu, su kuma ba da gudunmawa don warware wannan rikici a siyasance bisa kudurin MDD da yarjejeniyar wanzar da zaman lafiya a kasashen Labarawa da sauran matsaya daya da aka cimma. (Amina Xu)