in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
MDD ta yi kira da a hana tsananta halin da Palasdinu da Isra'ila ke ciki
2018-05-30 10:56:56 cri

Mai shiga tsakani na musamman a shirin wanzar da zaman lafiya a yankin gabas ta tsakiya na MDD Mista Nickolay Mladenov ya yi kira ga bangarorin daban-daban na Palasdinu da Isra'ila da su yi hakuri da juna don hana kara tsananta hali da ake ciki a tsakaninsu.

Nickolay Mladenov wanda ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar a jiya, ya kuma bayyana damuwa matuka kan harin bam da aka kai kudancin Isra'ila daga zirin Gaza, yana mai cewa, ba za a lamunci wannan mataki ba ko kadan, kuma zai kawo barazana ga kokarin da kasashen duniya ke yi na kyautata halin da ake ciki a zirin.

Ya kara da cewa, kamata ya yi bangarorin daban-daban masu ruwa da tsaki na Palasdinawa da 'yan Isra'ila, da su yi hakuri don kaucewa hasarar rayuka.

Rundunar tsaron Isra'ila ta sanar a jiya cewa, an kai harin rokoki fiye da guda 20 a yankin Eshkol dake dab da zirin Gaza, yayin da na'urar kakkabo makaman Isra'ila suka yi nasarar kakkabe galibinsu.

Jaridar nan ta Time of Israel ta ba da labari cewa, a kalla makaman roka 28 ne suka fada a yankin Isra'ila, lamarin da ya yi raunana mutum daya. A wannan rana da dare kuwa, sojin Isra'ila sun kai wasu jerin hare-hare kan makaman da Palasdinu ta girke a Gaza.

Hukuma kula da aikin ba da ilmi na zirin Gaza ta ba da sanarwa cewa, bam din da Isra'ila ta jefa ya fadi kan wata makaranta dake yankin yayin da dalibai suka yi jarabawa, lamarin da ya tayar da hankulan daliban, amma har yanzu babu mutane ya yi asara ba. (Amina Xu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China