in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An tabbatar da mutuwar mutane 5 sanadiyyar barkewar cutar kwalara a Nijeriya
2018-07-03 09:04:46 cri

Dan majalisar dokokin jihar Katsina Ahmed Abubakar, ya ce mutane 5 sun mutu, yayin da wasu 50 ke kwance a asibiti sanadiyyar barkewar cutar kwalara a yankin Funtua na jihar.

Ahmed Abubakar ya shaidawa manema labarai cewa, ana zargin mutanen da suka kamu da cutar, sun sha gurbatacciyar ruwa saboda shigowar lokacin damina.

Dan majalisar ya kuma yi kira ga ma'aikatar kiwon lafiya ta jihar, ta gaggauta aikewa da kwararru zuwa yankin domin dakile bazuwar cutar ga sauran sassan jihar.

Barkewar cutar kwalara dai ta zama wani al'amari dake faruwa a jihar a kowacce shekara, domin mazauna yankunan karkara kan samo ruwa ne daga koguna ko madatsan ruwa, musammam a lokacin damina. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China