Obadiah Moyo, ya ce gwamnati da majalisar gudanarwa ta birnin Harare da 'yan sanda, na iyakar kokarin takaita yaduwar cutar da ta barke makonni 2 da suka gabata a yankunan Glen View da Budiriro masu yawan jama'a.
Tun daga lokacin ne kuma, cutar da ake samu daga ruwa mara tsafata, wadda aka ayyanawa matakin ta-baci, ta yadu zuwa sauran sassan kasar.
An samu barkewar cutar ne sanadiyyar fashewar bututun kawar da najasa, wanda ya bata ruwan rijiyar burtsatsai da wasu daga cikin mazauna yankunan ke amfani da shi.
Ministan ya ce suna kara kai ruwa da magunguna yankunan da cutar ta barke, biyo bayan tallafin da suka samu daga abokan hulda daban-daban.
A cewar Ministan kananan hukumomi July Moyo, la'akari da yanayin bukatar gaggawa na lafiya, tuni ma'aikatarsa ta shawarci shugaban kasar Emmerson Mnangagwa ya ayyana matakin ta baci kan annobar. (Fa'iza Mustapha)