in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban Sin ya yi kira da a ci gaba da daukar matakan karfafa hadin gwiwar kasar sa da Afirka ta kudu
2018-07-25 19:25:39 cri

A jiya Talata ne shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya bayyana bukatar kara karfafa kawancen dake wanzuwa tsakanin kasar sa da Afirka ta kudu, domin kaiwa ga cimma nasarar ci gaban sassan biyu.

Shugaba Xi ya ce akwai tarin alfanu game da alakar dake akwai tsakanin kasashen, don haka ba za a saurara ba, har sai an kai ga nasarar da aka sanya gaba. Kaza lika a cewar sa, yayin da kasashen biyu ke bin hanyar neman bunkasuwa, ya zama wajibi a kara azama wajen taimakawa juna, ta yadda za a kai ga cimma biyan bukata.

Shugaban na Sin na wannan tsokaci ne, yayin liyafar maraba da takwaransa na Afirka ta kudu Cyril Ramaphosa ya shirya masa, a wani bangare na cikar dangantakar diflomasiyyar kasashen biyu shekaru 20.

Xi ya kara da cewa, akwai bukatar sassan biyu su kalli babbar manufar alakar su, su kara inganta amincewa juna ta fuskar siyasa, kuma a ko da yaushe, su yi mu'amala da juna da sahihiyar zuciya, a matsayin abokai, kuma 'yan uwa da ke fatan za su gudu tare su tsira tare.

A nasa bangare, shugaba Ramaphosa ya jinjinawa irin kusancin da jam'iyyun dake mulki a kasashen biyu ke da shi, da al'ummun kasashen biyu, da ma kyakkyawar dangantakar diflomasiyyar su a matakin yanki da na kasa da kasa, yana mai cewa dangantakar Afirka ta kudu da Sin, na cikin wani mafi kyawun yanayi a tarihin ta.

Shugaban na Afirka ta kudu ya bayyana ziyarar shugaba Xi ta wannan karo, a matsayin wadda ta dara matsayin ta gama gari.(Saminu Alhassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China