Baya ga haka, rahoton ya kuma nuna cewa, dangantakar dake tsakanin Sin da Afirka na da kyau kamar yadda kafofin watsa labarun nahiyar Afirka ke kallo, kana yawan jarin da Sin ke zubawa a Afirka na karuwa. Rahoton ya ce, akwai tunanin bangarorin biyu za su karfafa hadin kai wajen yin cudanya a fannonin siyasa, manyan ayyuka, cinikayya, harkokin kudi da kuma kara fahimtar juna a tsakanin al'ummunsu da dai sauransu. (Bilkisu)