in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Yadda aka kalli kasar Sin daga nisan mita dubu 10 a sararin samaniya
2018-09-17 16:46:51 cri
An gudanar da taron tattaunawa kan bunkasuwar kasar Sin na shekarar 2018 na kwanaki biyu a nan birnin Beijing a ranar 16 ga wata, inda wakilai kimanin 800 daga kamfanonin Sin da na waje, da masana da hukumomin gwamnatocin kasashen duniya suka bada shawarwari kan yadda za a yi kwaskwarima da bude kofa a sabon zamanin da ake ciki a kasar Sin. Farfesa Pieter Bottlier na jami'ar Johns Hopkins ta kasar Amurka wanda ya taba zama babban wakilin bankin duniya dake kasar Sin ya bayyana cewa, "ban yi aiki har na tsawon shekaru fiye da 20 a kasar Sin ba, don haka ra'ayina ya yi kamar ana kallon kasar Sin daga nisan mita dubu 10 a sararin samaniya, wato ke nan shi ne ra'ayin kasa da kasa". Irin wannan ra'ayi ne ake bukata, musamman a lokacin da ake fuskantar matsaloli ta fannin dunkulewar kasashen duniya bai daya, da kariyar ciniki da kuma yanayin rashin tabbas a duniya a lokacin shekaru 40 da fara yin kwaskwarima a cikin gida a kasar Sin da bude kofa ga waje.

Me aka gano a yayin da ake kallon kasar Sin daga nisan mita dubu 10 a sararin samaniya?

Da farko, an ga nasarori da imani da aka samu a kasar Sin, wannan shine tushen kasar Sin na gudanar da harkokinta da kanta. A cikin shekaru 40 da suka gabata, Sin ta shiga harkokin duniya tare da samun nasarori. Tsohon shugaban bankin duniya Robert Bruce Zoellick mai halartar taron tattaunawar ya bayyana cewa, ya gano nasarorin da Sin ta samu, ya kuma nuna yabo ga kokarin jama'ar Sin da imaninsu don samun nasara.

Ban da haka, mutane sun ga irin gibin da ake samu, gami da kalubalen da ake fuskanta, wannan ma ya zama dalilin da ya sa kasar Sin ta dau aniyar kara zurfafa yin gyare-gyare, da bude kofarta. Yanzu haka, matsalar data fi addabar kasar Sin ita ce bata samu isashen ci gaba ba a fannin tattalin arziki. Saboda har yanzu, matsakaicin ma'aunin GDP na kasar yana kan matsayi mizani na 70, tsakanin kasashe da yankuna fiye da 190 na duniyarmu. Haka kuma, zuwa karshen shekarar bara, akwai mutane fiye da miliyan 30 da suka ci gaba da fama da talauci a kasar, wadanda ke bukatar samun tallafi. Don haka, a nan gaba kasar Sin zata yi nazari kan hanyar da zata bi don raya tattalin arziki da zaman al'umma, gami da kokarin tabbatar da ingancinsu.

A ganin tsohon shugaban bankin duniya mista Robert Bruce Zoellick, yayin da kasar Sin ke cigaba da kokarin aiwatar da manufar gyare-gyare a gida da bude kofa ga kasashen waje, zata fuskanci manyan kalubaloli guda 3, wadanda suka kunshi yadda za a tabbatar da samun ci gaba mai dorewa, wanda ya shafi bangarori daban daban, da yadda ake kallon tasirin da kasar Sin take samarwa duniya. Ban da haka kuma, ya dora muhimmanci kan yadda kamfanoni masu zaman kansu ke samar da gudunmowa ga ci gaban tattalin arzikin kasar ta Sin a shekarun baya. Hakika kamfanoni masu zaman kansu sun taba taka muhimmiyar rawa game da tattalin arzikin kasar Sin har ma sun samar da kashi 70% na karuwar tattalin arzikin kasar. Sai dai a yanzu, kamfanoni masu zaman kansu da sauran kamfanonin iri daban daban, dukkansu na bukatar samun wasu matakan gyare-gyare daga gwamnatin kasar, don tabbatar da samun ci gaba mai inganci, gami da tinkarar kalubalolin da ake fuskanta.

A karshe dai, kyakyyawar makoma da kuma cimma moriyar juna ne aka gano, wadanda kuma su ne tushe ga kasar Sin da sauran kasashen duniya wajen samun cigaba tare. A shekaru 40 da suka gabata, adadin tattalin arzikin kasar Sin bai wuce kashi 1.8 bisa dari cikin karfin tattalin arzikin duniya ba, kana adadin ya karu zuwa kashi 15 bisa dari a shekarar 2017 da ta gabata, kuma cikin shekaru da dama da suka gabata, kasar Sin tana bada gudummawa ta kashi 30 bisa dari kan karuwar tattalin arzikin duniya a ko wace shekara.

A matsayinta na kasa mafiya fitar da hajojinta ga kasashen duniya, da kuma kasa ta biyu wajen shigar da hajoji daga ketare, kasar Sin ta bada gudummawa matuka ga kasashen duniya bisa ci gaban tattalin arzikin data samu. Shugaban reshen kamfanin mota na BMW na kasar Jamus dake kasar Sin Jochen Goller ya bayyana cewa, kasuwannin kasar Sin muhimman kasuwanni ne ga kamfanonin motoci na kasa da kasa, a shekarar 2017, kamfanin BMW ya sayar da motoci guda dubu 560 a kasar Sin, adadin da ya wuce motocin da aka sayar dasu a kasashen Amurka da Jamus baki daya.

Kuma bisa wani sabon binciken da aka yi kan kamfanonin kasar Amurka sama da guda 430 dake kasar Sin, an ce, duk da irin matsalolin da takaddamar ciniki tsakanin kasar Sin da kasar Amurka ta haifar musu, amma kashi 2 bisa 3 a cikinsu, ba su kaurar da na'urorin kere-kere nasu daga kasar Sin ba, kuma ba za su yi hakan ba.

Tsohon babban masanin tattalin arziki na bankin duniya, Justin Yifu Lin, ya bayyana cewa, ana bukatar kasar Sin ta kara daukar nauyin dake rataye a wuyanta wajen kyautata tsarin neman bunkasuwa na duk duniya, da taimakawa sauran kasashe masu tasowa wajen samun ci gaba da kawar da fatara gami da samun moriya tare. Justin Yifu Lin ya nuna cewa, yayin da salon tattalin arzikin kasar Sin ke samun sauye-sauye, wato daga sana'ar ayyukan gona zuwa sana'ar kere-kere har zuwa tattalin arzikin da ya shafi sana'ar bada hidima, kasar ta Sin zata samar da guraben ayyukan yi miliyan 85 ga sauran kasashen dake tasowa ta hanyar gudanar da sana'ar kere-kere, al'amarin da babu shakka zai taimaka ga ci gaban sana'ar kere-kere a wadannan kasashe.

A wasu lokuta, kallon kasar Sin daga nisan mita dubu goma a sararin samaniya, ba za'a iya gani sarai ba ko kuma za'a iya yin kuskure wajen gani, amma za'a iya daidaita wadannan matsaloli ta hanyar kara yin mu'amala da taimakon juna. Ci gaba da aiwatar da manufar yin gyare-gyare a cikin gida da bude kofa ga kasashen waje, babbar matsaya ce da aka cimma a duk fadin kasar Sin. Ya kamata kasar Sin ta gudanar da harkokinta da kyau, hakan zai sanya Sin ta kara samun kyautatuwa da bunkasuwa, sauran kasashen duniya kuma zasu ci gajiya daga ci gaban da Sin ta samu.(Zainab Zhang, Bello Wang, Maryam Yang, Murtala Zhang, Lubabatu Lei)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China