in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin ta yi tir da 'yan sandan kasar Sweden da suka nuna karfin tuwo ga masu yawon shakatawa na Sin
2018-09-15 21:02:07 cri

A yau Asabar 15 ga wata, ofishin jakadancin Sin dake kasar Sweden, ya bayar da sanarwa game da batun 'yan sandan Sweden, wadanda suka nuna karfin tuwo kan masu yawon shakatawa Sinawa, lamarin da ya faru a farkon wannan wata, inda ya yi tir da wannan aiki, domin ya keta hakkin dan Adam, ya kuma kawo illa ga tsaron 'yan kasar Sin, kana ya bukaci gwamnatin kasar Sweden da ta yi bincike kan batun cikin hanzari, da amsa bukatun masu yawon shakatawar na yanke hukunci ga 'yan sandan, da neman gafara gare su, da kuma biyansu kudin diyya.

Bisa labarin da ofishin jakadancin Sin dake kasar Sweden ya bayar, an ce, da sanyin safiyar ranar 2 ga watan Satumba, Mista Zeng da iyayensa daga kasar Sin sun isa wani otel dake birnin Stockholm. Sabo da lokacin yin rajistar dakinsu bai yi ba, Mista Zeng ya bukaci biyan kudi ga otel din don neman baiwa iyayensa damar su huta a kujerar dake babban dakin baki na otel din, inda ya ce shekarun iyayensa sun zarce 60 don haka suna da bukatar hutawa. Amma bangaren otel din bai amince ba, kuma ya kira 'yan sanda domin daidaita batun. Bayan da 'yan sanda suka zo otel din, sai sun janyo Mista Zeng da iyayensa daga otel ta hanyar nuna karfin tuwo, suka kai su zuwa wani filin kaburbura dake da kilomita fiye da goma da birnin Stockholm, suka ajiye su a can. Ba yadda za su yi, sai Mista Zeng da iyayensa sun nemi taimako daga wajen mutane, sa'an nan sun samu damar koma birnin Stockholm. Daga baya kuma sun tuntubi ofishin jakadancin Sin dake kasar Sweden. Bayan hakan, ofishin jakadancin Sin da ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin sun yi fadi-tashi kan wannan batu ga gwamnatin kasar Sweden, amma ba ta mayar da martani kan batun ba, kana kafofin watsa labaru na Sweden ma sun yi shiru kan batun.

Sanin kowa ne, kasar Sweden wata kasa ce mai sukuni, wadda wai take kiyaye hakkokin bil Adama sosai kamar yadda ita kanta ta fada, har ma ta samar da "Rahoton hakkin dan Adam na duniya" a watan Mayu na shekarar 2017, inda ta ya yi tsegumi kan halin hakkin dan Adam da kasashe da dama ciki har da kasar Sin ke ciki. Ta mai da kanta a matsayin "Alkalin hakkin dan Adam na duniya". A matsayinsa na wani muhimmin bangare na ayyukan gudanar da harkokin kasa, yadda 'yan sanda na kasar Sweden suka gudanar da aikinsu na iya shaida matsayin ci gaban kasar Sweden. Amma abin da 'yan sandan birnin Stockholm suka yi da sanyin safiyar ranar 2 ga watan Satumba, ya sa mu yi shakku sosai kan matsayin kasar Sweden game da kiyaye hakkin dan Adam, da ma gudanar da aikin doka. Shin ta dauki ma'auni biyu a kan batun hakkin 'dan Adam ne? Wato ta kare hakkin jama'arta kawai, ga jama'ar sauran kasashe kuma, tana iya cin zarafinsu bisa son rai?

Ban da hakan, ya zuwa yanzu, sati biyu ke nan da faruwar wancan lamari, inda ofishin jakadancin kasar Sin da ke Sweden, da ma ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin suka nuna wa gwamnatin Sweden rashin jin dadinsu daya bayan daya, amma ba ta mayar da martani ko kadan ba. Lallai wannan bai dace da ladabin diflomasiyya ba. Bangaren 'yan sanda da ma mahukuntan Sweden, sun yi haka ne domin rashin girmamawa, ko domin neman kaucewa karbar kuskuren da ta yi? (Zainab Zhang, Kande Gao, ma'aikatan Sashen Hausa na CRI)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China