in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kyakkyawan zumuncin dake tsakanin shugabanni da al'ummomin Sin da Rasha
2018-09-14 15:57:02 cri
A yayin taron dandalin tattaunawar batun tattalin arziki na yankin gabashin duniya karo na 4 da aka kammala kwanan baya, shugaban kasar Sin Xi Jinping da takwaransa na kasar Rasha Vladimir Putin sun gana da juna, ganawar da ta kasance na uku cikin watanni hudu da suka gataba. A hakika, yadda shugabannin kasashen biyu suka sha ganawa da juna ya zama wata muhimmiyar alama ta huldar da ke tsakanin kasashen biyu. A hakika, cikin shekaru sama da biyar da suka gabata, shugaba Xi Jinping da shugaba Vladimir Putin sun gana da juna har sau sama da 20, lamarin da ya nuna kyakyyawar dangantaka dake tsakanin kasashen biyu, da kuma yadda kasashen biyu suka sanya muhimmanci a kan huldarsu ta fannin harkokin diflomasiyya.

Jagorancin shugabannin kasashen biyu sun kara karfafa huldar da ke tsakanin kasashensu. Yadda shugabannin kasashen biyu suka sha ganawa da juna, tare da bullo da tsare-tsare ga ci gaban huldar abokantaka a tsakanin kasashensu, sun taimaka ga ci gaban huldar kasashen biyu. Baya ga haka, yadda shugabannin kasashen biyu suka yi ta kokarin shirya manyan bukukuwa da shirye-shirye a tsakaninsu ma ya taimaka ga ci gaban hadin gwiwarsu.

A kokarin da shugabannin suka yi, huldar da ke tsakanin kasashen biyu sun shiga wani sabon yanayi na samun inganci da saurin ci gaba. Baya ga kyautatuwar tsarin ciniki a tsakaninsu, kasashen biyu sun kuma ingiza jerin shirye-shiryen da suka shafi zuba jari da makamashi da sufuri da manyan ayyuka da sauransu, har ma an gano sabbin fannonin da suka fara hadin gwiwa, ciki har da kimiyya da ayyukan gona da ciniki ta yanar gizo da sauransu.

Cudanyar jama'a na da muhimmanci wajen yin mu'ammala tsakanin kasashe. Shugabannin kasashen biyu sun fahimci muhimmiyar rawar da mu'ammala a tsakanin jama'arsu za ta taka sosai, idan har ana son kafa tushe sosai na ra'ayin jama'a, za a iya kafa babban gini na sada zumunta a tsakanin kasashen Sin da Rasha daga zuriya zuwa zuriya. A watan Yulin bara, shugaba Xi da shugaba Putin sun sa hannu kan wata hadaddiyar sanarwa game da zurfafa dangantakar abokantaka ta hadin kai bisa manyan tsare-tsare a dukkan fannoni a tsakanin jamhuriyar jama'ar kasar Sin da tarrayar kasar Rasha a birnin Mosccow, inda suka jaddada cewa, yin mu'ammala tsakanin jama'a da yin cudanyar al'adu muhimmin sashe ne na sada zumunta a tsakanin kasashen biyu daga zuriya zuwa zuriya.

A yayin taron dandalin tattaunawar harkokin tattalin arziki na gabashin duniya karo na hudu da aka shirya a ranar 12 ga wata, shugaba Xi Jinping ya bayar da wani labari game da cudanyar jama'ar kasashen biyu: cibiyar All-Russian Children's Center "Ocean" dake Vladivostok ta taba karbar yara sama da 900 da suka bukata daga bala'in girgizar kasa da ta faru a birnin Wenchuan na lardin Sichuan na kasar Sin, wadannan yara sun samu kulawa sosai a cibiyar, har sun sada zumunta sosai da Rasha. Wani daga cikinsu mai suna Xi Junfei ya bayyana fatansa na yin karatu a Rasha idan ya girma. Yanzu kuma ya cimma burinsa, yana karatu a jami'ar gabas mai nisa ta Rasha mai suna Far Eastern Federal.

Haka kuma, bisa jagorancin shugabannin biyu, zumuncin dake tsakanin kasar Sin da kasar Rasha ya samu goyon bayan al'ummominsu matuka. Kana, al'ummomin kasashen biyu suna ci gaba da karfafa mu'amala da fahimtar juna a tsakaninsu, sakamakon wasu shirye-shiryen yin mu'amala da aka yi tsakanin kasashen biyu, kamar shekarar al'adun Sin na kasar Rasha, da kuma shekarar al'adun Rasha na kasar Sin, shekarar mu'amalar matasa a tsakanin kasar Sin da kasar Rasha, da kuma shekarar mu'amala da hadin gwiwar wurare daban daban a tsakanin kasashen biyu da dai sauransu.

A shekarar 2017, Sinawa masu yawon shakatawa kimanin miliyan 1.7 sun ziyarci kasar Rasha, yayin da 'yan Rasha fiye da miliyan 2.3 suka zo yawon bude ido a kasar Sin. Ban da haka, Ya zuwa karshen shekarar 2016, yawan daliban kasar Sin da suke karatu a Rasha hadi da yawan daliban Rasha da ke neman samun karin ilimi a kasar Sin, ya kai fiye da dubu 70, adadin da ake sa ran ganin karuwarsa zuwa dubu 100 a shekarar 2020. Yanzu a kasar Sin, a duk wani kantin sayar da littattafai, za a iya samun littattafan da wasu shahararrun marubutan kasar Rasha, irinsu Pushkin da Tolstoy, suka rubuta cikin sauki. Sa'an nan a kasar Rasha, yayin da shugabannin Sin da Rasha suka gana a garin Vladivostok, an nuna wani wasan kwaikwayon da masu fasahar al'adu na kasar Sin suka tsara, a cikin gidan nuna wasannin kwaikwayo na Mariinsky da ke birnin St Petersburg na kasar Rasha.

Hakika huldar dake tsakanin kasashen Sin da Rasha abin koyi ne ga sauran kasashe, musamman ma ta fuskar kulla hulda tsakanin manyan kasashe dake makwabtaka da juna. Wannan hulda mai kyau, ta kuma shaida nasarar da kasar Sin ta samu, a kokarinta na yin hulda da sauran kasashe. Ta la'akari da sakamakon da aka samu a wannan fanni, za a fahimci cewa, kalaman da Wang Yi, mamban majalisar zartaswar kasar Sin kana ministan harkokin wajen kasar, ya fada, tana bisa turba, inda Wang ya fadi cewa, bisa niyyar da shugabannin kasashen Sin da Rasha suka nuna ta kyautata huldar dake tsakanin kasashen 2, jama'ar kasashen na ta kokarin kulla kauna da samun fahimtar juna tsakaninsu, abin da ya rika karfafa huldar dake tsakanin kasashen 2.(Lubabatu Lei, Bilkisu Xin, Bello Wang, Maryam Yang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China