Da yake tsokaci game da hakan, jakadar Amurka a MDD madam Nikki Haley, wadda kuma ta nemi a yi shiru na dan lokaci, domin jimamin asarar rayukan da aka yi shekaru 17 da suka gabata, ta ce duk da cewa an shafe tsawon lokaci tun bayan aukuwar hare haren, amma har yanzu duniya na jin radadin asarar rayukan da aka yi.
Kimanin mutane 3,000 ne suka rasa rayukan su, bayan da wasu mahara suka yi garkuwa da wasu jiragen sama, wadanda daga bisani suka yi amfani da su wajen kutsawa cikin wasu manyan gine-ginen dake biranen New York, da Washington D.C. da kuma jihar Pennsylvania. (Saminu Alhassan)