Wata sanarwar da mahukuntan kasar suka fitar ta bayyana cewa, sakamakon kazantar da al'amura ya sa majalisar zartarwar gwamnatin hadaka ta ayyana dokar ta baci ta gaggawa a Tripoli, babban birnin kasar da nufin kare rayukan fararen hula da dukiyoyin gwamnati da na sassa masu zaman kansu.
Sanarwar ta kara da cewa, gwamnati ba za ta lamunci yadda ake karya dokoki da matakan tsaro a birnin na Tripoli ba, don haka yanayin na bukatar daukar dukkan matakan tsaro da na soja gami da na fararen hula da suka wajaba.
Rahotanni na cewa, tun a ranar Litinin din da ta gabata, kudancin birnin Triploli ke fuskantar tashin hankali tsakanin gwamnati da dakaru masu dauke da makamai, lamarin da ya kai ga mutuwar mutane 41 kana wasu 123 kuma suka jikkata. (Ibrahim Yaya)