Sashen kula da masu fama da raunuka na ma'aikatar lafiyar kasar ya bayyana cikin wata sanarwa cewa, tashin hankalin Tripoli yayi sanadiyyar rayuka 78 da kuma jikkata mutane 210.
Sanarwar tace kawo yanzu an riga an sallami mutane 103 daga asibiti bayan an duba lafiyarsu, kana wasu mutanen 16 sun bace.
A baya bayan nan birnin Tripoli yana fuskantar tashin hankalin wanda ya kaure tsakanin sojojin gwamnati da mayaka runduna ta 7 a kusa da birnin Tarhuna, mai tazarar kilomita 80 a kudu maso gabashin Tripoli.
A ranar Alhamis, ofishin MDD dake Libya ya sanar da cewa bangarorin da basa ga maciji da juna sun rattaba hannu kan yarjejeniyar tsagaita bude wuta da nufin kawo karshen tashin hankalin da ya barke, wanda yayi sanadiyyar raba magidanta 1,800 da matsugunansu.
Tun bayan tashin hankalin da ya barke a shekarar 2011 wanda yayi sanadiyyar kifar da gwamnatin tsohon shugaban kasar Muammar Gaddafi, Libya take cigaba da fuskantar tashe tashen hankula, da rudanin siyasa da rarrabuwar kawuna a tsakanin jama'ar kasar.