in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An yi kira ga kasashen Afirka da su fadada cinikayya tsakanin su
2018-09-14 10:29:25 cri
Masana a fannin tattalin arziki, sun yi kira ga kasashen Afirka da su dauki karin matakai na fadada cinikayya da juna, muddin dai suna da burin cin gashin kai a fannin nan da shekaru 5 masu zuwa.

Masanan wadanda suka gudanar da wani taro a jiya Alhamis a birnin Nairobin kasar Kenya, sun yi amannar cewa, Afirka na shigo da kayayyaki daga kasashen wajen nahiyar, saboda karancin cinikayya da suke yi da juna.

Da yake tsokaci game da hakan, shugaban hukumar bunkasa fitar da hajoji zuwa kasashen waje na kasar Kenya Jaswinder Bedi, ya ce akwai bukatar sauya yadda nahiyar ke gudanar da al'amura.

Mr. Bedi ya ce Afirka ba za ta samu cikakken 'yanci a fannin tattalin arziki irin na kasashen Asiya da Turai da Amurka ba, har sai ta sauya salon gudanar da cinikayyar ta.

Kwararru a fannin cinikayya daga ciki da wajen kasar Kenya, sun tattauna, tare da musayar shawarwari tsakanin su, a taron da aka yiwa lakabi da "Gina tsarin cinikayya tsakanin kasashen Afirka da gudummawar kasar Kenya", inda suka maida hankali ga zakulo dabarun inganta cinikayya tsakanin kasashen Afirka.

Wasu alkaluman kididdiga da bankin raya harkokin shige da ficen hajoji na Afirka ko Afreximbank ya fitar, sun nuna cewa daya daga muhimman dalilan da ya sanya cinikayya tsakanin kasashen Afirka ke ja da baya, shi ne karancin musayar bayanai na kasuwa da cinikayya tsakanin kasashen nahiyar.

A yanzu haka cinikayya tsakanin kasashen nahiyar bai wuce kaso 15 bisa dari ba, yayin da na nahiyar da Turai ke da kaso 59 bisa dari, sai kuma kaso 51 bisa dari dake tsakanin nahiyar ta Afirka da Asiya. (Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China