Cikin wata sanarwa da ta aike ga taron masu jiragen ruwa da ya gudana a Sychelles, Manajar Daraktan bankin wadda ke kula da harkokin cinikayya a tsakanin kasashen Afirka, Kanayo Awani, ta ce rashin kyawun hanyoyin sufuri na ruwa na illa ga cinikayya a nahiyar, tana mai cewa a yanzu nahiyar ce ta fi kashe kudi a harkar sufuri a duniya.
Ta ce kasashen Afrika kalilan ne suka samar da hanyoyin sufuri na ruwa da suka dace, duk da cewa sufuri ta ruwa ne ya mamaye kaso 92 na cinikayyar nahiyar.
A cewarta, kamata ya yi a samar da shirye-shiryen bada kwarin gwiwa domin karfafawa 'yan kasuwa nahiyar taimakawa raya sufurin jiragen ruwa.