in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ministocin wajen kasashe mambobin AU sun gana a Addis Ababa
2018-09-13 10:49:39 cri
Ministocin harkokin wajen kasashe mambobin kungiyar hadin kan Afirka ta AU, sun gudanar da wani taro na yini biyu a birnin Addis Ababan kasar Habasha, game da nazartar ci gaban da ake samu, ta fuskar sauye sauye da ake burin aiwatarwa a tsarin gudanarwar kungiyar.

Ministocin sun fara taron ne a ranar Talata, a helkwatar kungiyar. Ana kuma fatan taron zai zamo wani dandalin nazartar manyan sauye sauye, da kallo na tsanaki game da kalubale da ake fuskanta, tare da tantance hakikanin sakamako da aka cimma a fannin gudanar da sauye sauyen.

Kaza lika ana fatan taron zai zamo wata dama ta share fage, ga babban taron jagororin kungiyar dake tafe cikin watan Nuwamban karshen shekarar nan, wanda zai guda a birnin na Addis Ababa.

Da yake tsokaci game da hakan, babban shugaban hukumar zartawar kungiyar ta AU Moussa Faki Mahamat, ya ce tun bayan fara aiwatar da sauye sauye ga tsarin gudanar da kungiyar, an cimma manyan nasarori. Wasu daga irin wadannan nasarori sun hada da daidaita tsarin ayyukan majalissar shugabannin kasashe mambobin ta, da inganta tsarin ayyuka, da karfafa ma'amala tsakanin ta da hukumomin raya tattalin arziki na yankunan nahiyar Afirka, ta yadda ayyukan su za su ci gaba da gudana cikin managarcin tsari, wanda zai taimaka ga cimma muradun ci gaban nahiyar. (Saminu Alhassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China