in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Matasan Afirka sun nuna rashin gamsuwa kan matsalar da ake fuskanta a fannin samun rance don raya aikin gona
2018-08-22 10:18:41 cri
Samari da 'yan mata masu kamfanonin aikin gona na kasashen Afirka sun nuna rashin gamsuwa kan matsalar da suke fuskanta a fannin neman rance, wadda a ganinsu na hana ci gaban ayyukansu na raya aikin gona.

Sun bayyana haka ne a ranar Talatar da ta gabata, a wajen wani taron da aka kira a gefen bikin matasa na Afirka dake gudana a birnin Kigali, fadar mulkin kasar Rwanda. Taron mai taken "Samar da guraben aikin yi ga matasa a fannin aikin gona a matsayin wani matakin da zai taimaka wajen kawar da yauwa da talauci a nahiyar Afirka".

Kasar Rwanda ce ta karbi bakuncin taron tsakanin ranekun 20 zuwa 21 ga watan Agustan da muke ciki, inda aka dora muhimmanci kan yunkurin sanya matasan Afirka don su shiga a dama da su a kokarin sauya tsare-tsaren aikin gona, musamman ma ta hanyar fasahar sadarwa ta zamani, da fasahohin kula da kamfani.

A wajen taron, Dieudonne Twahirwa, shugaban Gashora Farm Ltd, wani kamfani mai sarrafa yaji dake kasar Rwanda, ya ce a matsayinsa na matashi mai kula da kamfani, yana fama da wahalhalu wajen samun rance daga banki, ganin yadda kudin ruwa ya yi yawa, kana ana bukatar wasu kadarori da za a dogara da su kafin a iya samar da rance. (Bello Wang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China