in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Masana sun yi kira ga kasashen Afrika su mayar da hankali ga kyautata kunshin kayakinsu
2018-09-12 10:36:14 cri
Masana a Afrika, sun ce akwai bukatar 'yan kasuwar nahiyar, su mayar da hankali sosai wajen kyautata kunshi da tambarin kayakinsu, domin ba su damar yin takara a kasuwar duniya.

Masanan sun ce kunshe kayayyaki da kyau na da muhimmin tasiri ga kara ingancin abinci da sauran kayakin da Afrika ke samarwa wajen inganta shigarsu takara.

Wata sanarwa da aka fitar a gefen taron kasa da kasa kan inganta fitar da kayyayaki zuwa kasashen ketare dake gudana a Lusaka babban birnin Zambia, ta ce kwararrun sun ce rashin kunshe kayyakin da kyau na haifarwa nahiyar Afrika dimbin asara.

A cewar George Okech, wakilin hukumar samar da abinci da kula da ayyukan noma ta duniya FOA a Zambia, rashin kunshe kayayyaki da kyau na daya daga cikin manyan matsalolin da masu kanana da matsakaitan sana'o'in kayakin gona ke fuskanta, wadanda kuma su ne ke sarrafa kayaki mafi yawa da ake samarwa a nahiyar.

Ita kuwa mataimakiyar Daraktan zartarwa na hukumar kula da cinikayya ta duniya Dorathy Tembo, cewa ta yi, abun takaici ne yadda batun kunshe kayyaki ya ja hankalin kafafen yada labarai a baya bayan nan saboda wasu dalilai, kuma yadda yake taimakawa wajen gurbata muhalli ya haifar da mummunan tunani a wajen masu sayen kayayyakin. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China